Alhamis 2 Yuli 2026 - 18:25
Ayoyin Gina Rayuwa | Gargadi Daga Alkur'ani: Mantawa Da Allah Shi Ne Mafarin Rushewar Dan Adam

Hauza / Mantawa da Allah shi ne mafarin rugujewar ruhin ɗan adam, wanda hakan ke kai shi ga mantawa da kansa. Kamar yadda ya zo a aya ta 19 a cikin Suratul Hashr, mutumin da ya manta da Allah, sakamakon sabo da barna, yana jefa kansa a cikin wani rami na halaka wanda karshensa ba a sani ba. Komawa zuwa ga tafarkin gaskiya yana bukatar kasancewar Allah a cikin kowane lokaci na rayuwa da kuma gujewa aikata zunubai.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, za mu riƙa kawo muku shirin "Ayoyin Da Ke Gina Rayuwa"; wanda ya ƙunshi tarbiyyar ayoyin Alkur'ani mai girma tare da takaitaccen bayani mai amfani ga rayuwar yau da kullum don samun rabo.

Jawabin Hujjatul Islam wal Muslimin Abbas Ashja'i Isfahani:

Ma'aunin Daidaita Yanayin Ruhin Dan Adam

{وَلَا تَکُونُوا کَالَّذِینَ نَسُوا اللَّهَ فَأَنسَاهُمْ أَنفُسَهُمْ ۚ أُولَٰئِکَ هُمُ الْفَاسِقُونَ}

"Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta da Allah, sai Ya mantar da su kansu. Waɗannan su ne fasiƙai." (Suratul Hashr: 19)

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai. Wannan aya ta 19 a cikin Suratul Hashr tana magana ne a kan "muhimmin batu na mantawa da kai".
Wannan aya mai girma tana ba da "ma'aunin duba yanayin ruhin ɗan adam" kuma tana zama gargadi mai tsanani game da "sakamakon mantawa da Allah".

1. Dangantaka Tsakanin Mantawa da Allah da Mantawa da Kai

Da farko, babban darasin wannan aya shi ne gargadin da Alkur'ani yake mana idan muna son mu duba kanmu da kuma kwatanta kanmu da wasu: "Kuma kada ku kasance kamar waɗanda suka manta da Allah". A ci gaban ayar kuma yana cewa: "Sai Ya mantar da su kansu". Wato mantawa da Allah yana kai wa ga mantawa da kai. Wannan alaƙa ta kai-tsaye tsakanin mantawa da Ubangiji da mantawa da kai, darasi ne mai zurfi kwarai da gaske.
Saboda haka, idan mutum yana son ya tantance ko ya manta da kansa ko a'a, da kuma ina matsayinsa yake sannan kuma ko yana kan hanyan kwarai, to ya duba ya gani: Shin ya manta da Allah a rayuwarsa, ko kuwa yana sanya tsoron Allah a cikin dukkan lamuransa? Idan ya ga ya zama kamar waɗanda ba sa la'akari da Allah a cikin harkokin rayuwarsu, to ya sani cewa lallai ya manta da kansa.

2. Sanin Kai Shi Ne Mafarin Sanin Allah

Wani muhimmin abu a cikin wannan aya shi ne cewa tafarkinmu na zuwa ga Allah yana farawa ne daga sanin kai. Kamar yadda ya zo a shahararren hadisi:

«من عرف نفسه فقد عرف ربه»

"Wanda ya san kansa, to lallai ya san Ubangijinsa."

Muna kai wa ga sanin Allah ne ta hanyar sanin kanmu. Saboda haka, mantawa da kai yana farawa ne kuma yana samo asali ne daga mantawa da Allah.

3. Waɗanda Suka Manta da Allah Su Ne Fasiƙai

Darasi na gaba a cikin wannan aya yana nuni ne ga abubuwan da ke kai mutum ga mantawa da Allah da kuma mantawa da kansa. A karshen ayar ya ce: "Waɗannan su ne fasiƙai".

Fasikanci, barna, zunubi, da bin tafarkin Shaiɗan su ne ke sa mutum ya manta da Allah. Daga cikin siffofin waɗanda suka manta da Allah akwai nacewa wajen aikata sabo da laifuka.

Kammalawa

Babban darasin da za a koya daga wannan aya shi ne: Idan muna son mu kasance da Allah a rayuwarmu, dole ne mu nisanci sabo. Idan kuma kaddara ta sa aka kai ga aikata sabo, to dole ne a gaggauta yin tuba domin kada mantawa da Allah ta kai mu ga mantawa da kanmu; domin mantawa da kai tana jefa mutum a gangaren halaka wanda karshensa ba a sani ba.

Ba za a sani ba ko mutum zai cika da kyau ko a'a, kuma a wane yanayi zai bar wannan duniya. Don haka, dole ne ɗan adam ya kasance mai ambaton Allah da tunawa da Shi a kowane lokaci na rayuwarsa domin ya samu kansa, kuma insha Allahu, kada ya fada cikin ramin mantawa da kai.
 

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha